Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyoyi biyar na zawarcin Silva, Chelsea tana son ɗauko Havertz da Benrahma
Chelsea ta yi amannar cewa dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, zai koma Manchester United don haka yanzu ta mayar da hankali wurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz. (ESPN)
A gefe guda, Chelsea ta tuntubi kungiyar wacce take buga Gasar Bundesliga domin yiwuwar dauko dan wasan mai shekara 20 Havertz, a yayin da ake rade radin cewa shi ma dan wasan Brentford Said Benrahma yana cikin wadanda Chelsea take son daukowa. (Guardian)
Aston Villa ta dade tana son dauko dan kasar Algeria mai shekara 24 Benrahma kuma za ta yi kokarin sayensa - idan ta kauce wa fadawa kasan teburin Gasar Premier. (The Athletic)
Dan wasan Brazil Thiago Silva yana son ci gaba da zama a Turai bayan da aka gaya masa cewa ba za a sabunta kwangilarsa a Paris St-Germain ba, kuma ya yi amannar cewa zai iya buga tamaula a kungiyar akalla tsawon kakar wasa biyu masu zuwa. (ESPN)
Kungiyoyin kwallon kafar Turai biyar - Arsenal, Everton, Newcastle, West Ham da kuma Wolves - suna son dauko dan wasan na PSG mai shekara 35. (90 Minutes)
Arsenal tana fatan dangantakarta da mahaifin Pierre-Emerick Aubameyang - wanda kuma shi ne wakilin dan wasan mai shekara 30 - za ta taimaka mata wajen sabunta kwangilarsa kyaftin din nata. (Telegraph)
Leicester City tana son dauko dan wasan Ajax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila Ben Chilwell, wanda ake sa ran zai koma Chelsea ko Manchester City. (Mirror)
Manchester United ba ta son dan wasan Wales Daniel James, mai shekara 22, ya bar kungiyar don zaman aro - ko da kuwa ta dauko dan wasan Ingila Sancho. (Manchester Evening News)
RB Leipzig ta gwammace ta sayar da dan wasan Faransa mai shekara 21 Dayot Upamecano, wanda ake rade radin zai koma Arsenal, maimakon ta bayar da aronsa ba tare da ta karbi ko sisi ba idan kwangilarsa ta kare a watan Yunin 2021. (Bild)
Dan wasanParis St-Germain Idrissa Gueye ya ce ba shi da niyyar barin kungiyar, duk da cewa PSG za ta bar dan kasar Senegal mai shekara 30 ya kama gabansa idan yana so. Ana hasashen zai koma daya daga cikin kungiyoyin Gasar Premier, inda aka ce Wolves da tsohuwar kungiyarsa Everton suna zawarcinsa. (Le10Sport)
An bai wa Barcelona wa'adin zuwa ranar 7 ga watan Yuli domin ta biya euro 110m don dauko dan wasan Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez idan ba haka ba za a fasa sayar mata shi. (Sky Sports)