Ƙalubalen da Messi zai fuskanta idan an ci gaba da La Liga

Ranar Alhamis za a ci gaba da gasar La Liga ta bana tun bayan da aka dakatar da wasanni a watan Maris, saboda tsoron yada cutar korona.

Ranar Asabar Barcelona za ta yi wasan mako na 28, inda za ta ziyarci Real Mallorca.

Saboda haka Barcelona da Lionel Messi na shirin fuskanta kalubale da zarar an ci gaba da wasannin kakar shekarar nan.

Barcelona na fatan lashe kofin La Liga na uku a jere da kuma Champions League, shi kuwa Messi na fatan samun nasarori na kashin kansa.

Lashe kyautar Pichichi ta bakwai jumulla

Kyaftin din Barcelona shi ne na daya a cin kwallo a gasar La Liga mai 19 a raga da tazarar biyar tsakaninsa da Karim Benzema na Real Madrid.

Hakan na nufin Messi na shirin lashe kyautar wanda ke kan gaba a cin kwallo a La Liga kuma na bakwai jumulla wato kyautar Pichichi.

Wannan bajintar zai sa Messi ya haura Pedro Telmo Zarraonandia wanda ya ci kyautar zama na daya a yawan cin kwallaye a La Liga mai guda shida.

Shi dai Telmo Zarra dan kasar Spaniya ya yi kusan rayuwar wasan tamaula a Athletico Bilbao daga 1940 zuwa 1955 wanda ya ci kwallo 335.

Dan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a kungiya

Dan wasan tawagar Brazil, Pele wanda ya ci kwallo 643 shi ne ke kan gaba a tarihin wanda ya ci kungiya kwallaye da yawa a tarihi.

Messi yana da 627 da ya ci wa Barcelona, kuma hakan na nufin saura 17 dan kwallon na Argentina ya kafa nasa tarihin.

Sauran wasa 12 a karkare gasar La Liga da sauran wasanni nan gaba da Messi zai buga tunda da sauran kwarinsa har yanmzu babu wanda ya san iya kwallayen da zai zazzaga a raga a tarihi.

Idan har Messi yana daga cikin 'yan wasan da Barcelona za ta ci kofin La Liga na bana na kuma uku a jere to zai kafa wasu tarihin.

  • Messi zai zama na biyu da ya yi nasarar cin kofin Zakarun Turai na biyar kenan, zai zama saura daya ya yi kan-kan-kan da Gento mai shida a tarihi.
  • Zai kuam ci kofin La Liga na tara a shekara 12 kenan kuma na 11 daga 16 da aka fafata da shi aka ci kofin.
  • Lionel Messi ya kofi 34 a Barcelona, idan ya ci La Liga da Champions League a bana zai yi kan-kan-kan da Ryan Giggs tsohon dan wasan Manchester United mai guda 34 a kungiya daya.