Gwamnatin Burtaniya ta amince a koma Gasar Firimiya ba 'yan kallo

Za a ci gaba da gudanar da gasar wasanni na cikin gida ba tare da 'yan kallo ba daga ranar Litinin ɗin nan, a cewar gwamnatin Burtaniya.

Ƙa'idojin sassauta kullen 'mataki na uku' ne suka share hanyar komawa harkokin wasanni kai tsaye daga ranar 1 ga watan Yuni a karon farko tun cikin tsakiyar watan Maris.

Yanzu ya rage wa ɓangarorin wasanni daban-daban su ƙiyasta irin kasadar da ke akwai, a tuntuɓi masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da koci-koci da sauran ma'aikatan da ke tallafa wa 'yan wasa.

A ranar Litinin za a ci gaba da gasar tseren dawaki da wasan sunuka, amma ita Gasar Firimiya sai ranar 17 ga wata za a koma.

Manyan ƙungiyoyin wasa a Ingila har sun koma atisaye a kan 'mataki na biyu' na tsarin sassauta dokokin kulle a ranar 25 ga wannan wata.

A ranar Asabar, Gasar Firimiya ta tabbatar cewa babu ɗan wasa ko ma'aikacin da ke tallafa wa 'yan wasa da aka samu ya kamu da cutar korona bayan gwajin da aka yi wa mutum 1,130 daga ranar Alhamis zuwa juma'a.

Zuwa yanzu mutum 12 ne suka kamu da cutar a cikin gwaji 3,882 da aka yi wa ɓangarorin da ke da ruwa a gasar.

"Zaman jira ya ƙare. Nan gaba kaɗan harkokin wasanni kai tsaye a Burtaniya za su dawo cikin aminci da kuma yanayi da aka iyakance shi cikin tsanaki," a cewar Sakataren harkokin Dijital, Al'adu, Yaɗa labarai da Wasanni, Oliver Dowden.

"Waɗannan ƙa'idoji da aka shimfiɗa za su samar da wani amintaccen tsari da za a ci gaba da gasar wasanni ba tare da 'yan kallo ba."

Da yake ƙarin haske yayin jawaban kullu-yaumin na Gwamnatin Burtaniya kan annobar korona, Oliver Dowden ya kuma ce: "Ƙwallon ƙafa, wasan tenis da tseren dawaki, tseren motocin Fomula Wan da wasan kurket da golf da ƙwallon zari-ruga, da sunuka da sauransu duk sun shirya dawowa kan allunan talbijin ɗinmu nan gaba kaɗan."