Kasuwar saye da musayar 'yan ƙwallo: Makomar Sane, Hernandez, Hendrick, Bellingham

Asalin hoton, PA Media
Bayern Munich ta nemi bai wa Manchester City dan wasanta mai shekara 24 dan kasar Faransa Lucas Hernandez domin karbo dan wasan City dan kasar Jamus, Leroy Sane, dan shekara 24. (TZ - via Manchester Evening News)
Dan wasan Argentina Mauro Icardi, 27, yana shirin komawa Paris St-Germain dindindin bayan ya amince da yarjejeniyar £51.2m da Inter Milan. (Sky Sports)
AC Milan ta nuna sha'awar karbo aron dan wasan Burnley da Jamhuriyar Ireland Jeff Hendrick, mai shekara 28. (Sky Sports)
Wakilin dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 21 Achraf Hakimi, wanda kungiyar ta karbo aro daga Real Madrid, ya ce Madrid ce babban abin da ke gabansa - ko da yake ya ce dan kasar ta Morocco ba ya gaggawar komawa can. (Evening Standard)
Leicester City ta kara kaimi a yunkurinta na dauko dan wasan Celtic mai shekara 22 dan kasar Norway Kristoffer Ajer. (Nicolo Schira, via Leicestershire Live)
KocinBirmingham City Pep Clotet yana sa ran za a ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiya Jude Bellingham idan aka koma Gasar Zakarun Turai, a yayin da ake rade radin Manchester United da Borussia Dortmund suna son dauko dan wasan dan shekara 16. (Sky Sports)
Arsenal ta kammala sayen dan wasan Norway dan asalin Rwanda George Smith, mai shekara 19. (VG - in Norwegian)
KazalikaArsenal ta sabunta sha'awar dauko dan wasan Lyon da Faransa Moussa Dembele, dan shekara 23, kuma tuni ta tuntubi wakilinsa. (L'Equipe - in French)











