La Liga: Za a ci gaba da gasar kwallon Spaniya a ranar 11 ga watan Yuni

Asalin hoton, Getty Images
Za a koma fafatawa a gasar La Liga ta kasar Spaniya a ranar 11 ga watan Yuni, in ji shugaban gasar Javier Tebas.
Sannan ya bayyana cewa za a soma gasar kwallo ta kaka mai zuwa a 12 ga watan Satumba.
"Mun kammala shiri kuma akwai mahimmanci a karkare gasar," Tebas ya shaidawa gasar jaridar Marca ta Spaniya.
A ranar Asabar, Firayi ministan Spaniya, Pedro Sanchez ya bada dama ga masu shirya gasar kwallon kafa a kasar cewa za su iya koma wa fagen tamaula tun daga ranar 8 ga watan Yuni.
Tuni 'yan wasan gasar ta La Liga suka soma atisaye gabanin ci gaba da gasar.
A ranar 12 ga watan Maris ne aka dakatar da gasar La Liga saboda cutar Korona.
A yayin da ya rage wasa 11 a kammala gasar, Barcelona ce kan gaba inda ta baiwa Real Madrid tazarar maki biyu.







