Shin ko Hazard zai kare martabar Real idan an ci gaba da La Liga?

Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya wuce ne Firai Ministan Spaniya, Pedro Sanchez ya ce za a ci gaba da gasar La Liga ta bana ranar 8 ga watan Yuni, amma ba 'yan kallo.

Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasanni a Spaniya, bayan bullar cutar korona.

An dai tsaya a wasannin mako na 27 a gasar La Liga, kuma karawar karshe da aka yi ita ce wanda Real Sociedad ta je ta doke Eibar 2-1 a kwantan mako na 24 ranar 10 ga watan Maris.

Wani dan wasan da ke fatan taka rawar gani da zarar an koma La Liga ta 2019-20, bai wuce Eden Hazard ba wanda ya warke daga jinya da ya yi.

Real Madrid ta sanar da daukar Eden Hazard ranar 7 ga watan Yunin 2019 daga Chelsea kan Yuro miliyan 100.

Kungiyar ta ce kunshin yarjejeniyar dan wasan tawagar Belgium zai kai Yuro miliyan 146, zai kuma dinga karbar albashin fam 400,000 a kowanne mako.

Tun da Real ta gabatar da shi gaban magoya baya, dan wasan ya kasa hawa kan ganiyarsa kamar yadda ya yi kaurin suna wajen taka leda.

Ranar 14 ga watan Satumba ya fara buga wa Real wasa na minti 30 a fafatawa da Levante.

Daga nan ne ya nuna mahimmancin sayensa da aka yi da rawar da zai taka a Real Madrid.

Daga nan sai komai ya canja bayan da Paris Saint Germain ta ziyarci Real Madrid ranar 26 ga watan Nuwamba, inda Hazard ya fadi ya ji rauni a Champions League.

Daga nan Real Madrid ta saka shi a wasa ranar 16 ga watan Fabrairu a gasar La Liga a wasa da Celta Vigo, bayan da ya yi jinyar kwana 67.

Bayan da ya ci gaba da wasa sai ya kara rauni a dai wajen da ya yi na farko a fafatawa da Levante a gasar La Liga.

Ranar 5 ga watan Maris Real ta tura Hazard zuwa Dallas domin likitoci su yi masa aiki, inda aka ce zai yi jinyar wata uku.

Bullar cutar korona ta sa an dakatar da dukkan wasanni a Spaniya, hakan ya bai wa Hazard murmurewa har ake sa ran zai buga wa Real wasa da Eibar idan an ci gaba da gasar La Liga cikin watan Yuni.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona wadda ke jan ragamar teburin.