Haaland zai iya kai wa matsayin Ronaldo - Rivaldo

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon gawurtaccen dan kwallon Brazil, Rivaldo ya ce matashin dan kwallon Norway, Erling Haaland zai koma gasar La Liga kuma watakila Real Madrid ce za ta zama kungiyarsa.
A cikin watan Junairu Haaland ya koma Borussia Dortmund daga kungiyar Red Bull Salzburg kuma ana alakanta shi da Madrid.
Matashin mai shekaru 19, ya zura kwallo 10 cikin wasanni 9 da ya bugawa Dortmund.
Rivaldo ya ce Haaland zai haskaka sosai a gasar La Liga kuma zai iya kai wa matsayin irinsu Ronaldo na Brazil.
"A yanzu haka babban dan wasa ne, kuma zai iya zama zakara a duniya", Rivaldo ya rubuta a shafin Betfair.
"Wasu na kwatantashi da Ronaldo Nazario saboda irin gudunsa da saurinsa wajen murza leda."







