Haaland ya ci uku rigis a wasansa na farko a Dortmund

Asalin hoton, Getty Images
Dan kasar Norway mai shekara 19 mai taka wa Dortmund leda, Erling Braut Haaland, ya bai wa masu nuna shakku kansa kunya a ranar Asabar da kwallo uku rigis da ya zazzaga a ragar FC Augsburg a wasansa na farko.
Haaland wanda rahotanni suka rika alakanta shi da Manchester United da kuma Juventus, ya ci kwallo takwas a zagayen rukuni na gasar Champions League ta bana - shi ne na biyu wajen zira kwallaye a gasar.
Matashin dan wasan ya koma Dortmund kan fan miliyan 17 a watan da ya gabata bayan ya ci wa Red Bull Salzburg kwallo 28 a wasa 22 da ya buga wa Red Bull Salzburg a kakar bana - ciki har da uku rigis da ya ci sau biyar.
Yanzu haka ya ci na shida bayan ya taso daga benci kuma ana cin Dortmund 3-1. Ya ci daya kafin daga baya Jadon Sancho ya mayar da wasa 3-3.
Haaland ya ci ta hudu ana saura minti 18 wasa ya kare a wani fasin da Thorgan Hazard ya ba shi.
Kyaftin Marco Reus ne ya sake ba shi kwallo, inda bai yi wata-wata ba ya ci ta 5 kuma wasa ya tashi 5-3.
"Na ji dadi sosai da cin wadannan kwallaye kuma na kasa gano dalilin hakan," dan wasan dan gidan tsohon dan wasan Manchester City, Alf-Inge Haaland, ya fada jim kadan bayan tashi daga wasan.
"Na zo kulob mai girma kuma mai cike da mutanen kirki. Na zo ne domin na zira kwallaye kuma na ji dadin wasana na farko."
Dortmund tana matsayi na hudu tare da Bayern Miunich a teburin Bundesliga da maki 33 kowaccebsu, maki bakwai tsakaninsu da RB Leipzig wadda take a saman teburin.












