Aubameyang zai buga wa Madrid, Arsenal ta fuskanci matsala kan Upamekano

Dan wasan Arsenal dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, ya yi wa kakansa alkawarin kafin ya mutu cewa zai buga tamaula Real Madrid, a cewar Sun.

Arsenal ta fuskanci gagarumin koma-baya a yunkurin da take yi na dauko dan wasan RB Leipzig dan kasar Faransa mai shekara 21, Dayot Upamecano bayan wakilinsa ya ce ba za a saki kudi masu yawa a kansa ba saboda annobar korona. (Sport 1, via Metro)

Shanghai Shenhua tana sa ran dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, zai koma murza mata leda idan ya kammala zaman aron da yake yi a Manchester United kafin a soma gasar Super League ta China, wacce za a fara a watan Yuli. (Sky Sports)

A gefe guda, Manchester United tana son sake gwada sa'arta a yunkurin da take yi na karbo dan wasan Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22. (Sport, via Mail).

Tottenham da Arsenal sun samu kwarin gwiwa a kokarinsu na sayo dan wasan Brazil Willian saboda Chelsea ba za ta tsawaita kwangilar dan kwallon mai shekara 31 ba. (football.london)

Borussia Dortmund tana son dauko matashin dan wasan Chelsea Charlie Webster sannan ta yi masa abin da ta yi wa Jadon Sancho. (Sun)

Kocin Chelsea Frank Lampard ya bi Dries Mertens a shafin Instagram kuma rahotanni sun ce ya tuntubi dan wasan na Belgium da Napoli, mai shekara 33, kai tsaye. (Express)

Shugaban Lyon Jean-Michel Aulas ya amince cewa zai yi wahala su iya rike manyan 'yan wasansu a bazara - a yayin da rahotanni suke cewa Chelsea tana son dauko dan wasansu dan kasar Faransa mai shekara 23 Moussa Dembele. (Star)

Manchester City tana zawarcin dan wasan Paris St-Germain dan kasar Faransa mai shekara 17, Edouard Michut. (Sky Sports)

Mahaifin dan wasan Brazili Gerson ya yi ikirarin cewa Arsenal da Tottenham suna son dauko dan wasan mai shekara 22 daga Flamengo. (ESPN, in Portuguese)