Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ta tsara yadda 'yan wasan La Liga za su koma atisaye
Mahukuntan gasar La Liga na tsara hanyar da kungiyoyi za su koma yin atisaye cikin gaggawa da zarar gwamnatin Spaniya ta amince.
A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a Spaniya don gudun yada cutar korona.
Mahukuntan gasar La Liga sun tsara hanyoyi da dama kan yadda 'yan kwallo ya kamata su fara atisaye, inda suka karkata kan matakan kare lafiya da zarar gwamnati ta amince.
Hakan zai bai wa mahukuntan damar ci gaba da gasar La Liga a tsakiyar Yuni ba tare da yan kallo ba, domin a karkare kakar 2019,20.
Kawo yanzu saura wasa 11 a kammala kakar shekarar nan, bayan da Barcelona ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.
Gwamnatin Spaniya ta tsara mataki hudu da za ta bi kan ta cire dokar hana fita waje tun daga 4 zuwa 11 ga watan Mayu, inda take sa ran fara atisaye daga lokacin.
Daya daga tsare-tsaren da mahukuntan La Liga suka yi har da fara atisaye na 'yan wasa daidaiku, sannan a koma yi cikin rukuni da na kungiya gabaki daya.
Kuma sai an gwada lafiyar 'yan wasa da masu horas da su kan a fara atisaye don dakile yada cutar.