Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Celtic da Copenhagen: Michael Santos ba zai buga wasa uku ba
Dan wasan FC Copenhagen Michael Santos ba zai buga wasa uku ba, bayan da Uefa ta dakatar da shi kan cin zarafin wani a lokacin Europa League da suka doke Celtic.
'Yan Sandan Scotland sun tuhumi Santos da kungiyarsa Copenhagen kan cin zarafin jami'in tsaro a lokacin da suke murnar kwallo na biyu da suka ci a karawar da suka yi nasara da ci 3-1 a Glasgow a watan Fabrairu.
Rahoto na cewar wani ne ya ture dan sanda a lokacin da 'yan wasan kungiyar Denmark ke murna cin kwallo a wasan zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a Europo League.
Copenhagen ta ce wani jami'i ne ya rike Pep Biel wanda ya ci mata kwallon, ita kuwa Celtic cewa ta yi wani mai kula da da'ar 'yan kallo ne ya yi kokarin hana hatsaniya daga baya aka yi waje da shi.
Santos ya buga wa Copenhagen karawar da ta yi a Basaksehir a Instanbul a zagayen kungiyoyi takwas da suka rage a Europa League, amma yanzu ba zai buga wasa uku nan gaba ba.