Coronavirus: Likitoci sun sallami Marouane Fellaini bayan jinya

Marouane Fellaini

Asalin hoton, Marouane Fellaini

Bayanan hoto, Marouane Fellaini ya koma taka leda a China a 2019 bayan shekara shida da ya yi a Manchester United

Tsohon dan wasan Manchester United mai wasan tsakiya, Marouane Fellaini, wanda ya kamu da coronavirus ya koma gida, bayan da likitoci a China suka yi jinyarsa.

Dan wasan na tawagar kwallon kafar Belgium ya yi jinyar mako uku, bayan da ya kamu da annobar ranar 22 ga watan Maris.

Dan wasan ya rubuta a shafinsa na sada zumunta a Instagram cewar ''Lokaci ya yi da ya kamata na yi godiya ga likitocin da suka duba lafiyata.''

Fellaini ya kuma yi godiya da kungiyarsa Shandong Luneng, wadda ta kula da shi kamar yadda ya kamata.

Kafafen yada labarai a China sun ce an kwantar da Fellaini a Asibitin Jinan wanda ya kware wajen yakar cututtka masu yaduwa.

A lokacin da yake jinya ya saka bidiyonsa yana motsa jiki a kafar sada zumunta.

Fellaini ya koma China ida taka leda a shekarar 2019 bayan shekara 11 da ya yi a Ingila tare da kungiyar Manchester United da kuma Everton.