Ba zan sayar da Kane a Ingila ba - Levy

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harry Kane ya zura kwallo 11 cikin wasanni 20 a kakar bana

Kungiyar Tottenham Hotspur ta ce bata da niyyar sayar da Harry Kane a karshen kakar wasan bana ko kuma a sayar da shi ga wata kungiya a Ingila.

Kane mai shekaru 26,ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru shida tare da Spurs a watan Yunin 2018.

Shugaban kungiyar, Daniel Levy ya ce zai iya sayar da shi a kan fan miliyan 200.

Manchester United ta kwana biyu tana zawarcin kyaftin din na Ingila.

Akwai bayanai da ke nuna cewa saboda matsalolin kudi, watakila Levy ya sayar da Kane idan har aka samu kungiyar da ta bayar da fan miliyan 200 daidai da kudin da PSG ta biya Barcelona saboda sayen Neymar a shekara ta 2017.