An ci gaba da buga gasar tamaula a Burundi

Burundi Football

Hukumar kwallon kafar Burundi FFB ta bayar da umarnin ci gaba da buga gasar kasar, bayan da ta tsara matakan hana yada coronavirus.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da gudanar da wasanninta idan har annobar ba ta yadu kamar wutar daji ba a Burundi.

Hukumar ta cimma wannan matsayar bayan taro da ta gudanar da kungiyoyin da ke buga wasannin.

Sai dai an umarci 'yan wasa da kada su yi murnar cin kwallo da rungumar juna, sannan su bayar da tazara tsakaninsu da alkalan wasannin.

Haka kuma an bukaci 'yan kwallo su wanke hannayensu kafin su shiga fili kuma babu gaisawa da juna da abokan kwallo da kuma alkalan wasa.

Shugaban hukumar kwallon kafar Burundi, Ndikuriyo Reverien ya shaida wa BBC cewar ya kamata su karasa sauran wasannin gasar da suka rage, amma idan coronavirus ta fantsama cikin kasar daga nan ne za su dakata.

Sauran wasannin mako uku suka rage a karkare gasar Burundi wadda take Gabashin Afirka wacce mutane uku daga miliyan 10 suka kamu da coronavirus kawo yanzu.

Burundi daya ce daga kasashe hudu da a duniya ke ci gaba da buga gasar tamaula, bayan Belarus, Nicaragua da Tajikistan.