Za a soke gasar Champions da ta Europa ta bana

Asalin hoton, Getty Images
Watakila a soke gasar Champions League da ta Europa ta bana idan ba a shawo kan coronavirus zuwa watan Satumba ba.
Shugaban hukumar kwallon kafar Uefa, Aleksander Ceferin ne ya bayyana haka, sai ya ce gwara a karasa wasannin ba tare da 'yan kallo ba maimakon a soke kakar bana.
Kawo yanzu dai an dakatar da dukkan wasannin Champions League da na Europa sakamakon tsoron yada coronavirus.
Kungiyar Manchester City da Chelsea na buga Champions League, yayin da Manchester United da Wolverhampton ke fafatawa a Europa League.
Tuni Uefa ta dakatar da wasannin karshe na cin kofin Champions League na maza da na mata da na Europa da ya kamata a karkare a cikin watan Mayu.







