Man Utd na son sayen Maddison, Liverpool ba za ta sake daukar Coutinho ba

Mai yiwuwa Manchester United ta mayar da hankalinta kan dan wasan tsakiya na Leicester City da Ingila James Maddison, mai 23, bayan dan wasan da ta dade tana zawarci kuma kyaftin din Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, ya ji rauni amma ba a filin kwallo ba. (Daily Star)

Liverpool ba ta sha'awar sake daukar dan wasan tsakiya na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, wanda yake Bayern Munich wadda ta yi aronsa daga Barcelona. (Mirror)

Real Madrid na sanya ido sosai kan sabon 'Kaka' na Sao Paulo Igor Gomes, mai shekara 21, yayin da Barcelona,Sevilla da kuma Ajax su ma suke son dauko dan wasan na Brazil mai buga gasar Under-20. (AS)

Dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, yana sha'awar ci gaba da buga gasar Firimiya idan ya bar Stamford Bridge, abin da ya sa Arsenal da Tottenham suka shiga shirin zawarcinsa. (ESPN Brazil - in Portuguese)

Arsenal, Tottenham da kuma West Ham na son dauko dan wasan Liverpool Dejan Lovren, mai shekara 30, bayan da Anfield ta nuna rashin sha'awar sabunta kwantaragin dan kasar ta Croatia. (Teamtalk)

Dan wasan da Arsenal ta yi aronsa Dani Ceballos, mai shekara 23, ya gwammace komawa Real Betis a kan ci gaba da zama a Emirates Stadium, idan Real Madrid ba ta son dan kasar ta Spain. (Estadio Deportivo via Express)

A shirye kocin Burnley Sean Dyche yake ya kammala gasar Firimiya a bayan fage, a tsari irin na gasar 'Kofin Duniya' (Telegraph - subscription required)