Burnley za ta ci gaba da biyan ma'aikatanta

Asalin hoton, BBC Sport
Kungiyar Burnley ta ce za ta ci gaba da biyan ma'aikatanta a lokacin nan da aka dakatar da buga tamaula.
Sai cikin watan Afirilu ake sa ran ci gaba da gasar Premier League, wadda aka dakatar saboda coronavirus.
Babban jami'in kungiyar, Neil Hart ya ce abu mafi mahimmaci shi ne su kula da dawainiyar ma'aikatansu da iyalansu a wannan halin da aka shiga.
Burnley tana ta 10 a kan teburin Premier, a lokacin da aka dakatar da wasannin shekarar nan, sakamakon coronavirus, kuma saura wasa tara a karkare kakar bana.
Ranar Laraba, Brighton da Bournemouth suka yi alkawarin bayar da tikitin kallon wasa 1,000 ga ma'aikatan lafiya da zarar an koma buga gasar Premier.
Haka kuma Brighton tana daga cikin kungiyoyin Premier da suka bai wa dubban mutane marasa galihu abinci, bayan da aka dage wasannin Premier.







