Wasannin Zakarun Turai da coronavirus ta shafa

Roma ta ce ba za ta je Sevilla buga wasan Europa ba wanda, aka tsara zai gudana ranar Alhamis saboda ba a bai wa jirginsu damar sauka a Sifaniya ba.

Tuni aka yanke hukuncin buga wasa zagayen 'yan 16 na gasar ta Europa ba tare da 'yan kallo ba saboda tsoron cutar yaduwar cutar Covid-19.

A ranar Talata, Atalanta ta kasar Italiya ta buga wasan Champions League da Valencia ba tare da 'yan kallo ba kamar yadda aka tsara.

A ranar Talatar dai hukumomin Sifaniya suka hana duk wani jirgi shiga kasar daga Italiya, amma Uefa ta roki a kyale jirgin Roma.

Sai dai a ranar Laraba gwamnatin Sifaniya ta ki amincewa da wannan roko.

A gefe daya kuma, Getefe ta ce ba za ta je Italiya ba a ranar Alhamis domin buga wasanta na Europa da Inter Milan.

A Faransa an dage wasan karshe na French League Cup tsakanin Paris St-Germain da Lyon, wanda tun da farko aka tsara yi ranar 4 ga watan Afirilu, an daga shi saboda tsoron coronavirus.