Atletico na zawarcin Lacazette, an yi wa Mbappe gwajin coronavirus

Atletico Madrid na ci gaba da nuna sha'awar dauko dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 28, daga Arsenal. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Barcelona ta ce dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 24, shi ne na biyu a cikin jerin 'yan wasan da take son sayowa a bazara bayan dan wasan Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22. (Mundo Deportivo - in Spanish)

An yi wa dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, gwajin cutar coronavirus kafin wasan Zakarun Turai da Paris-St Germainta fafata da Borussia Dortmund - ko da yake gwajin ya nuna ba ya dauke da cutar. (L'Equipe - in French)

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana so ya taimaka wa kungiyar ta sayo Jude Bellingham daga Birmingham inda ya gana da dan wasan mai shekara 16 da iyayensa lokacin da suka ziyarci United ranar Litinin. (Star)

Dan wasanMonaco da Faransa Djibril Sidibe, mai shekara 27, ya ce yana son sauya matsayinsa daga na zaman aro zuwa wanda aka saya a Everton. (RMC Sport, via Liverpool Echo)

Har yanzuLiverpool na fatan sayo dan wasan Belgium Jeremy Doku, mai shekara 17, bayan yunkurin da suka yi a baya na sayo matashin dan wasan na Anderlecht ya ci tura. (Het Nieuwsblad, via Star)

Mai yiwuwa dan wasanChelsea Michy Batshuayi, mai shekara 26, ya koma Crystal Palace, inda rahotanni suka ce dan kasar ta Belgium na sha'awar zama a kungiyar ta London a yayin da yake so a yawaita sanya shi a wasa. (Star)

Real Madrid na son maye gurbin kocinsu Zinedine Zidane da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino ko kuma tsohon takwaransa naJuventus Massimiliano Allegri. (Marca - in Spanish)

Uefa na duba yiwuwar dakatar da gasarEuro 2020 zuwa shekara daya saboda fargabar coronavirus bayan kungiyoyin kwallon kafar kasashe da dama sun yi roko ta yi hakan. (Tuttosport - in Italian)

Arsenal na son sanya hannu a kwangilar dogon zango da dan wasan Ingila Bukayo Saka, mai shekara 18, a yayin da Manchester Unitedke zawarcinsa. (Express)

Kazalika Arsenalna son sayo dan wasan Leeds United Ben White, a yayin da Liverpool, Manchester United da kuma Leicester ke zawarcin dan wasan mai shekara 22. (Sun)

Bournemouth, Norwich, Leeds da West Brom na sha'awar sayo dan kwallon Jamhuriyar Ireland Josh Cullen, mai shekara 23, wanda ke murza leda a West Ham. (Mail)