Za a buga wasanni a Spaniya da Fransa babu 'yan kallo

Napoli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barcelona ta yi 1-1 da Napoli a wasan farko na Champions

Za a buga wasannin Spaniya a mataki biyun farko ba tare da 'yan kallo ba nan da mako biyu masu zuwa saboda cutar coronavirus.

Matakin zai fara aiki a ranar Talata, inda za a buga wasa tsakanin Eibar da Real Sociedad ba tare da magoya baya ba.

Hukumomin La Liga sun dauki wannan matakin ne a matsayin umarnin riga-kafi daga ma'aikatar lafiya ta kasar da kuma hukumar wasanni.

Ita kuma faransa ta ce za a ci gaba da buga wasannin ba tare da 'yan kallo ba har san nan da 15 ga watan Afirulu mai zuwa.

A ranar Lahadi gwamnatin Faransa ta sanar da hana duk wani taron mutane da ya haura mutum 1,000.

Haka shi ma wasan Barcelona na Champions da Napoli da za a buga a ranar 18 ga watan Maris za a buga shi ne babu 'yan kallo a filin wasa na Nou Camp.

"An dai dauki wannan tsattsauran matakin ne saboda dalilan kiyaye lafiya," in ji Joan Guix, jami'in hukumar lafiya ta Catalunya.

Wannan ne wasa na biyu tsakanin kungiyoyin Spaniya da Italiya da aka shirya yi ba tare da 'yan kallo ba, bayan wasan Valencia da Atlanta da za a yi ranar Talata.

Haka zalika wasannin Europa tsakanin Sevilla da Roma da kuma wasan Getefe da Inter Milan za su gudana a irin wancan yanayi.

Wasan Paris St-Germain da Dortmund na Champions da za a yi ranar Laraba shi ma zai gudana shiru.

Sannan wasan Manchester United da LASK a Austriya ranar Alhamis shi ma babu 'yan kallo zai gudana.