Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United da Club Bruges sun tashi kunnen doki
Club Bruges da Manchester United sun buga 1-1 a wasan zagayen farko na kungiyoyi 32 da suka rage a Europa League.
Club Bruges ce ta fara cin kwallo ta hannun Emmanuel Dennis tun farko farkon fara tamaula.
Daga baya ne United ta farke ta hannun Anthony Martial kuma na 14 da ya ci wa kungiyar a kakar bana.
Sabon dan kwallon da United ta dauko aro a Janairu, Odion Ighalo ya shiga karawar daga baya, amma dai bai nuna kansa ba.
A ranar 27 ga watan Fabrairu Club Bruges za ta ziyarci Manchester United a Old Trafford.
Manchester United za ta karbi bakuncin Watford ranar 23 ga watan Fabrairu a gasar cin kofin Premier.
Wasu sakamakon wasannin da aka yi:
- Sporting 3 : 1 Istanbul Basaksehir F.K
- FC Kobenhavn 1 : 1 Celtic
- Cluj - Romania 1 : 1 Sevilla
- Ludogorets Razgrad 0 : 2 Inter Milan
- Eintracht Frankfurt 4 : 1 Red Bull Salzburg
- Shakhtar Donetsk 2 : 1 SL Benfica
- Wolverhampton Wanderers 4 : 0 Espanyol
- Bayer 04 Leverkusen 2 : 1 FC Porto
- Apoel Nicosia 0 : 3 FC Basel 1893
- Olympiacos 0 : 1Arsenal
- AZ Alkmaar 1 : 1Lask Linz
- VfL Wolfsburg 2 : 1 Malmo FF
- AS Roma 1 : 0 KAA Gent
- Glasgow Rangers 3 : 2 Sporting Braga