Manchester United ta sake doke Chelsea

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 2-0 a wasan mako na 26 a gasar Premier da suka kara a Stamford Bridge.

United ta ci kwallon farko ta hannun Anthony Martial, sannan Harry Maguire ya kara na biyu.

Sau biyu Chelsea na zura kwallo a raga ta hannun Kurt Zouma da kuma Olivier Giroud, amma na'urar dake taimakawa alkalin wasa yanke hukunci, VAR na haramta su.

Wannan ne karo na uku da United ke cin Chelsea a kakar bana, bayan 4-0 da ta yi nasara a Old Trafford a gasar Premier cikin watan Agusta.

Haka kuma a karshen watan Oktoba United ta shiga Stamford Bridge ta ci Chelsea 2-1 ta kuma fitar da ita a League Cup.

Wannan ne karon farko da Manchester United ta ci Chelsea gida da waje a gasar Premier, tun bayan 1987/88.

Duk da wannan rashin nasarar da Chelsea ta yi tana ta hudu a teburin Premier da maki 41 da tazarar maki uku da United wadda ta koma ta bakwai da maki 38.

Manchester United za ta karbi bakuncin Watford a wasan mako na 27 a gasar Premier ranar 23 ga watan Fabrairu.

Ita kuwa Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan hamayya ranar 22 ga watan Fabrairu a Stamford Bridge.