Manchester United za ta dawo da Sanchez

Manchester United ta yanke shawarar dawowa da dan wasan gabanta Alexis Sanchez da ke zaman aro a Inter Milan na kasar Italiya domin ba shi dama karo na biyu. (Star).

Arsenal na sa ran Barcelona za ta tuntube ta kan sha'awar sayen dan wasan gabanta Pierre-Emerick Aubameyang. (Telegraph).

Kazalika United na shirin sabon tayi kan dan wasan tsakiyar Sporting Lisbon Bruno Fernandes kafin a rufe kasuwar cinakayyar 'yan wasa ranar Juma'a. (Guardian).

Ita kuwa Atletico Madrid na dab da sayen Edinson Cavani daga PSG. (ESPN).

Cinikin Mari da Arsenal ya rushe kuma tuni dan wasan ya koma Brazil abinsa. (ESPN)

A yanzu burin Arsenal din da ke birnin London shi ne ta sake neman kawo dan wasan a matsayin aro da nufin tabbatar da zamansa kungiyar dindindin. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen ya kammala gwajin lafiya, kuma kowane lokaci daga yanzu Inter Milan za ta gabatar da shi ga 'yan jarida.

Tottenham ta karbi fam miliyan 17 a kan dan wasan na kasar Denmark. (Sky Sports).

Manchester United da Arsenal da kuma Chelsea na neman dan wasan tsakiyar Juventus Emre Can. (Metro)

Ita ma Borussia Dortmund ta Jamus ta shiga sahun masu neman Can din. (Bild - in German)

Su ma 'yan bayan Tottenham biyu Danny Rose da Kyle Walker-Peters akwai yiwuwar su bar kungiyar kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ta Janairu. (Standard).

Zai yi wuya Real Madrid ta iya barin Dani Ceballos ya tafi Valencia kuma tana son dan wasan ya baro Arsenal inda yake zaman aro a yanzu. (Marca - in Spanish)