Barcelona ta kammala daukar Martin Braithwaite

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta kammala daukar dan kwallon Leganes, Martin Braithwaite, a kan fam miliyan 15.
Mahukuntan La Liga ne suka bai wa Barcelona damar daukar dan wasa cikin gaggawa, bayan da aka kammala cinikayyar 'yan kwallo.
Haka kuma ya biyo bayan da Ousmane Dembele zai yi jinyar wata shida, bayan raunin da ya yi a wajen atisaye.
Cikin dokar La Liga ta amince cewar idan dan kwallon kungiya ya ji raunin da zai yi jinya daga wata biyar zuwa sama, za ta iya neman izinin daukar wani dan wasa cikin gaggawa.
Haka kuma cikin kunshin yarjejeniyarsa, duk kungiyar da take son sayensa a lokacin da kwantiraginsa bai kare ba za ta biya fam miliyan 251.
Cikin dokar La Liga ta amince Barcelona ta dauki dan wasan da bai da kungiya ko mai wasa a Spaniya, amma ba zai buga mata gasar Zakarun Turai ba.
Braithwaite ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara hudu a Leganes a watan Yunin da ta wuce, bayan da ya yi wasannin aro a Middlesbrough a bara.
Dan wasan ya ci kwallo 27 tun komawarsa Leganes ciki har da guda shida da ya ci a League daga 18 da kungiyar ta zura a raga a bana.
Leganes tana cikin 'yan kasan teburi a La Liga, ta kuma rasa dan kwallon tawagar Denmark da ya yi wa wasa 39, bayan da Barcelona ta biya kunshin kwantiransa.Kwantiragin Braithwaite zai kare a Yunin 2024.











