La Liga: Barcelona ta rage tazara tsakaninta da Real

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta kamo Real Madrid a yawan maki bayan ta kwaci kanta da kyar 2-1 a hannun Getafe a wasan La Liga mako na 24.
Allan Nyom ne ya fara jefa wa Barcelona kwallo a raga amma sai na'urar VAR ta soke ta, cewa ya yi wa Samuel Umtiti keta.
Antoine Griezmann ne ya ci wa Barca daga wani fasin na kwararru da Lionel Messi ya ba shi.
Sai kuma Sergi Roberto da ya ci tasa daga kwallon da Junior Firpo ya ba shi.
Amma ba a tashi ba sai da Angel Rodriguez ya zira wa Barca kwallo daga yadi na 18.
Angel Rodriguez mai shekara 32, yana cikin 'yan wasan da Barcelona ke kokarin dauka a wani cinikin gaggawa idan hukumar La Liga ta yarda da bukatarta.
Getafe ta kusa farkewa amma Marc-Andre ter Stegen ya yi namijin kokari ya hana Angel cin ta biyu.
Real Madrid za ta kara da Celta Vigo ranar Lahadi kuma idan ta ci wasan za ta dawo da tazarar maki ukun tsakaninta da Barca.











