Arsenal da Chelsea na son sayo Isco, Pogba zai iya fuskantar matsala

Isco

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal da Chelsea na zawarcin, Isco, inda aka ce za su iya biyan £63m a kan dan wasan mai shekara 27, a yayin da Real Madrid ke neman kudi gabanin soma musayar 'yan kwallon kafa a bazara. (Sun)

Hukumar kwallon Firimiya za ta kara kaimi kan binciken da take yi wa Manchester City bayan matakin da Uefa ta dauka na dakatar da su daga shiga gasar Turai tsawon kakar wasa biyu masu zuwa.(Mirror)

Manchester City na fuskantar yiwuwar a rage musu maki a gasar Firimiya kuma za a iya tursasa musu buga wasan League Two bayan da aka haramta musu shiga gasar Turai, a cewar masana harkokin kwallon kafa. (Star)

Paul Pogba yana son barin Manchester United a bazara sai dai fatan dan wasan mai shekara 26 na barin kungiyar salin-alin zai iya fuskantar matsala saboda United na son a biya su £83m kafin su saki dan wasan. (Guardian)

Inter Milan na son zawarcin dan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, idan har suka saki Lauturo Martinez, mai shekara 22 a bazara. (Star)

Lazio ta bai wa dan wasan gaban Chelsea Olivier Giroud, mai shekara 33 kwantaragi ko da yake zai jinkirta daukar mataki zuwa kakar wasa mai zuwa sakamakon zawarcinsa da Tottenham ta soma yi lokacin musayar 'yan kwallo a watan Janairu. (Telegraph)

Dan wasan Leicester City James Maddison, mai shekara 23, yana son komawa Manchester United. (Manchester Evening News)

Dan wasan Manchester United Tahith Chong, mai shekara 20, na duba yiwuwar tayin da Inter Milan na komawa can a bazara. (Guardian)

Manchester United na tunanin sayo dan wasan Tottenham mai shekara 26, Eric Dier, a bazara. (Star)

Dan wasan da Crystal Palace ke son sayowa Joakim Maehle, mai shekara 22, has ya bayyana karara cewa zai koma kungiyar idan suka daddale. (Standard)

Arsenal na fuskantar hatsarin rasa Bukayo Saka, mai shekara 18, idan aka soma musayar 'yan kwallo a karshen kakar wasa mai zuwa a yayin da suke ja-in-ja game da sabon kwantaragin matsayin dan wasan. (Metro)