''Na tausaya wa Guardiola kan dakatar da su''

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ya tausaya wa Manchester City da 'yan wasanta kan dakatar da su da hukumar kwallon Turai, UEFA ta yi.
UEFA ta dakatar da Manchester City daga shiga gasar zakarun Turai zuwa kaka biyu, bayan da ta samu kungiyar da laifin karya ka'idar kashe kudin da ya kamata a kakar wasa.
City na shirin daukaka kara, kuma kwana 10 ne tsakani da ya kamata ta shigar a kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya wato CAS.
''Na kadu da na ji labarin, a wannan lokacin ina jin hukuncin ya taba su,'' in ji kocin dan kasar Jamus.
''Ban san yadda abin nan zai yiwuba - abin da zan iya cewa Manchester City karkashin Pep Guardiola na taka kwallo mai ban sha'awa. Kullum Ina sha'awar abubuwan da suke yi.
''A gaskiya na ji tausayin Pep da 'yan wasansa domin su basu aikata komai ba, babu wani laifi da suka yi. Kwallo kawai suke buga wa, kuma mai ban sha'awa da kayatarwa.
Manchester City za ta ziyarci Real Madrid a wasan zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai ta Champions League ranar 26 ga watan Fabrairu.
City tana ta biyu a teburin Premier da maki 51, bayan buga karawar mako na 25, za ta fafata da West Ham a kwantan wasa a satin da za mu shiga.











