Mourinho ya ce Tottenham na jiyo kanshin zuwa Champions League

Jose Mourinho ya ce kungiyarsa ta Tottenham na cikin kulob biyar da ke "jin kanshin damar" zama cikin 'yan hudun farko da za su je gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Spurs wadda za ta kara da Aston Villa ranar Lahadi, na matsayi na shida a teburi, maki hudu tsakaninta da Chelsea mai matsayi na hudu.

Tottenham ta je matakin ne bayan ta doke Manchester City da ci 2-0 a wasansu na karshe kafin hutun hunturu da aka yi.

Da yake magana a shirin Football Focus na BBC, Mourinho ya ce: "Da farko dai, ina hangen kungiyoyi da dama sama da yadda mutane ke tunani.

"Saboda Chelsea na ta hudu, Tottenham na ta biyar, Manchester United tana ta shida, muna jiyo kanshin wannan damar.

"Ina ganin mutane na mantawa cewa akwai manyan kungiyoyi - Wolves, Sheffield United, Manchester United, har da Arsenal, saboda haka ba wai nisa tsakaninmu da Chelsea ba ne kawai."

Mourinho ya karbi ragamar Tottenham ne a watan Nuwamba bayan an kori Mauricio Pochettino kuma a lokacin akwai tazarar maki 11 tsakaninta 'yan hudun farkon.

Yana yin wannan magana ne kafin hukumar kwallon kafar Turai Uefa ta dakatar da Man City shiga Gasar Turai, abin da ya janyo ake tunanin kungiya ta biyar a teburi za ta samu shiga Champions League.