An amince Man Utd ta sayo Dembele, Tottenham na shirin kawo Godfrey

An amince Manchester United ta sayo dan wasanLyon dan kasar Faransa Moussa Dembele, mai shekara 23, a kan £60m. (Star)

Kazalika an bai wa Chelsea kwarin gwiwa don sayo Dembele a yayin da shugaban Lyon Jean-Michel Aulas ya bayyana cewa za su "sayar da dukkan dan wasan da ke son barin kulob din". (Mail)

Tottenham na duba yiwuwar sayo dan wasan Norwich mai shekara 22, Ben Godfrey, a kan £50m. (Express)

Haka kumaTottenham na sha'awara sayo dan wasan Norwich Max Aarons, mai shekara 20, a yunkurinta na sayo 'yan wasan biyu daga kungiyar. (Express)

Spurs na nuna gaje hakurinsu a kan Eric Dier, mai shekara 26, inda kulob din ke son sayar da shi saboda yana jan kafa ajen sanya hannu a abon kwantaragi. (Mail)

Paris St-Germain na shirin biyan dan wasan Faransa Kylian Mbappe £41m a duk shekara a yunkurinsu na hana dan wasan barin kulob din zuwa tsohuwar kungiyar Real Madrid a 2021. (Mirror)

A bazarar da ke tafe ake sa ran PSG za ta sayo mai tsaron ragar Manchester United mai shekara 22, Dean Henderson, wanda ke can Sheffield Uniteda matsayin aro.(Mail)

Pep Guardiola ya yi ikirarin cewa Manchester City za ta iya sallamarsa daga aiki idan suka kasa doke Real Madrid a gasar Zakarun Turai. (Guardian)

Tsohon dan wasan Ingila Joleon Lescott ya gargadi dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, da kada ya koma Manchester United a bazara mai zuwa yana mai cewa ba su da tabbacin zuwa gasar Zakarun Turai. (Standard)

KocinWolverhampton Wanderers Nuno Espírito Santo, mai shekara 46, wanda Everton da Arsenal, ke son saya ba ya tattaunawa da kungiyar a halin yanzu kan sabon kwantaragi, duk da cewa nan da wata 16 kwantaraginsa.

The quality of 32-year-old Argentina forward Lionel Messi papers over the cracks at Barcelona, says his former club-mate Malcom, the 22-year-old Brazilian striker now at Zenit St Petersburg. (Marca)

A shirye Real Madrid take ta biya Inter Milan 120m domin sayo dan wasan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22. (TyC Sports)

Tottenham na shirin yin gagarumin biki don taya dan wasanta da ya fi zura kwallaye Jimmy Greaves idan zai yi murnar cikarsa shekara 80 a duniya kafin karawarsu da RB Leipziga gasar Zakarun Turai makon gobe. (Standard)