Makomar Sancho, Van Dijk, Dembele, Ake, Mertens, Vertonghen da Long

Jadon Sancho

Asalin hoton, EPA

Manchester United na fatan shiga gaban Chelsea inda za ta ware fam miliyan £120m ta karbo dan wasan gaba na Borussia Dortmund na Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19. (Mirror)

Liverpool na shirin sabunta kwangilar dan wasan bayanta na Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 28, inda za a dinga biyansa sama da £150,000 a mako. (Football Insider)

Manchester United na iya sabunta bukatarta kan dan wasan Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele. (L'Equipe, via Manchester Evening News)

Tottenham za ta ware fam miliyan £40 domin karbo dan wasan Bournemouth Nathan Ake, mai shekara 24, (Express)

Dan wasan gaba naNapoli da kasar Belgium Dries Mertens, mai shekara 32, damarsa ta komawa Ingila na karuwa inda Chelsea,da Manchester United da kuma Arsenal dukkaninsu ke farautar dan wasan. (Mail)

Chelsea na sa ido kan dan wasan Morocco Hakim Ziyech bayan ta kasa karbo dan wasan mai shekara 26 daga Ajax a watan Janairu. (Telegraph)

Ajax na tunanin karbo dan wasan baya na Tottenham da Belgium Jan Vertonghen, inda kwangilar dan wasan mai shekara 32 za ta kawo karshe a karshen kaka. (Guardian)

Manchester CitydaManchester Unitedda Liverpool da Atletico Madrid dukkaninsu na son dan wasan Verona da Albania Marash Kumbulla, mai shekara 20. (Gazzetta dello Sport, via Sport Witness)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya kalli wasan da Bayern Munich ta yi kunnen doki da RB Leipzig ranar Lahadi, inda yake da sha'awa kan dan wasan baya na Leipzig na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21. (Mirror)

Liverpool na sa ido kan dan wasan gaba Benficana Brazil Carlos Vinicius inda take sha'awar karbo dan wasan mai shekara 24. (O Jogo, via Sport Witness)

Arsenal na sa ido kan matashin dan wasan tsakiya na Faransa mai shekara 21 Pape Gueye, wanda ke murza leda a kungiyar Lig 2 Le Havre. (Mail)

Chelseada Arsenal da kuma Manchester United na farautar matashin mai tsaron raga mai shekara 17 na Ingila Brad Young daga Hartlepool. (Sun)