An yi wa Balotelli jan kati minti bakwai da shiga fili

An bai wa Mario Balotelli jan kati minti bakawi da shiga fili, bayan da ya canji dan wasa a karawa da Cagliari.

Tun farko an bai wa dan kwallon Brescia katin gargadi, bayan da ya yi wa Fabio Pisacane keta a gasar Serie A da suka tashi 2-2.

Hakan na nufin Balotelli ba zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa AC Milan ba a ranar Juma'a, sakamakon hukunta shi da aka yi.

Dan wasan mai shekara 29 ya ci kwallo biyar tun bayan da ya koma Brescia da taka leda a watan Agusta.

Kawo yanzu Balotelli ya karbi jan kati 13 a tarihin tamaularsa, kuma shi ne na biyu a manyan gasar Turai da ake sallama a fili a kaka hudu baya da dan kwallon Monaco Jemerson.

A baya dai shugaban Brescia, Massimo Cellino ya ce tsohon dan wasan Manchester City da Liverpool zai iya barin kungiyar a watan nan na Janairu, domin ba zai hana su faduwa ba.

Brescia tana ta 18 a kasan teburin Serie A, wadda take neman maki daya ta fice daga jerin 'yan karshe-karshe.