Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Chelsea ta sha kashi a hannun Newcastle
Newcastle ta doke Chelsea a mintin karshe na wasan Premier mako na 23.
Chelsea ce dai ta rike mafi yawan wasan amma hakan bai sa tawagar Lampard din ta ci kwallo ba.
Tammy Abraham ya buga kwallo waje daga gefen turke sannan mai tsaron raga Martin Dubravka ya bige harin da N'golo Kante ya kai masa.
Kafin a ci kwallon, masu masaukin bakin ne Newcastle suka kusa jefa kwallo a raga laokacin da Joelinton ya bugo turke da kwallon da ya saka wa kai a minti na 22.