Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yunkurin Man United na daukar Fernandes ya ci tura
Yunkurin Manchester United na daukar Bruno Fernandes daga Sporting Lisbon ya kakare saboda kungiyoyin sun kasa cimma matsaya kan farashin dan wasan.
Sporting Lisbon na bukatar yuro miliyan 80 kan dan wasan mai shekara 25, abin da United ta gaza biya.
Ana ci gaba da tattaunawa kan dan wasan da Tottenham ta taya shi kan yuro miliyan 45 a shekarar da ta gabata.
United ba ta yanke shawarar daina neman wasu 'yan tsakiyar ba yayin da take ci gaba da zabarin 'yan wasan da za ta dogara da su a tsakiyar fili.
Sai dai za ta ci gaba da duba 'yan wasan da suke kasuwa ne kawai a lokacin da mako biyu ya rage a rufe kasuwar ta saye da musayar 'yan wasan Turai.
United ta fada wa Sporting Lisbon cewa ba za a kulla wata yarjejeniya ba har sai ta rage farashin dan wasan.
Solskjaer da mataimakinsa Mike Phelan sun je kasar Portugal a ranar 5 ga watan Janairu, inda suka kalli yadda dan wasan ke taka leda a wasansu da FC Porto.
A ranar Lahadi Man United za ta yi tattaki zuwa Anfield domin karawar Premier mako na 23 tsakaninta da Liverpool.