Arsenal za ta yi bajinta karkashin Arteta

David Luiz

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron baya, David Luiz ya ce kungiyarsa za ta yi bajinta a kakar bana, bayan da Arsenal ta doke Manchester United ranar Laraba.

Arsenal ta doke da ci 2-0 a wasan mako na 21 da suka fafata a Emirates, kuma nasarar farko karkashin koci Mikel Arteta.

Sokratis Papastathopoulos da kuma Nicolas Pepe ne suka ci wa Gunners kwallayen, hakan ne ya mai da kungiyar ta 10 a kan teburi da tazarar maki hudu tsakaninta da United ta biyar.

Nasarar da Gunners ta yi ya kawo karshen buga wasa bakwai a gida wato filinta na Emirates ba tare da yin nasara ba.

Luiz, mai shekara 32, ya ce ya yi amannar cewa Arteta zai bunkasa salon takun ledar 'yan wasa da hakan zai kai su ga yin nasarori.

Luiz ya kara da cewar Arteta kwararren mai horas wa ne ya kuma san tamaula, zai dora kungiyar kan hanyar yin nasarori.

Tun bayan da Arsenal ta bai wa Arteta aikin kocinta, ya lashe wasa daya kenan da canjaras biyu da rashin nasara a karawa daya.