Premier League: Leicester ta tumurmusa Aston Villa har gida

Jamie Vardy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwallo 16 Vardy ya ci a kakar bana

Leicester City ta ragargaji Aston Villa har gida da ci 1-4 a wasan Premier mako na 16.

Wannan ce nasara ta takwas a jere da Leicester ta samu a Premier ta bana kuma karon farko kenan da kungiyar ke cin wasan Premier takwas a jere.

Jamie Vardy, kamar yadda aka saba, shi ne ya bude wasan da kwallon da ya ci a minti na 20 bayan ya yanke golan Villa, Tom Heaton. Ya kara ta biyu a minti na 75.

Vardy ya ci kwallo a wasa takwas a jere a kakar bana, rabon da hakan ta faru tun a 2015 lokacin da Vardy din da kansa ya ci a wasa 11 a jere - yanzu haka shi ne kan gaba wurin zira kwallaye a kakar bana da kwallo 16.

Dan Najeriya Kelechi Iheanacho ma ya ci kwallo a minti na 41 a wasan da aka fara da shi na farko a kakar bana. Ya ci kwallo hudu kenan a dukkanin wasa hudu da ya buga a bana ga Leicester City.

Jack Grealish ne ya ci wa Villa kwallo daya tilo a minti na 45+2, sai kuma Evans, wanda shi ma ya ci a minti na 49, wadda ita ce kwallonsa ta farko a kakar bana ga Leicester.

Leicester City na ci gaba da zama a matsayi na biyu da maki 38, maki takwas kenan tsakaninta da Liverpool a saman teburi.