Premier League: An kama mai kalaman wariya a wasan Manchester

Asalin hoton, Getty Images
An kama wani mutum daga cikin magoya bayan kwallon kafa da ya fito fili yana nuna kamalan wariya ga 'yan wasan Manchester United yayin wasan hamayyar Manchester da ya gudana a ranar Asabar.
'Yan sanda sun ce sun samu rahoton wani magoyin baya da ake zargi da nuna kalaman wariya yayin wasan.
Mutumin mai shekara 41, an kama shi ne saboda zargin karya dokar kalaman nuna wariya tare da tunzura wasu kuma har yanzu yana tsare a hannun 'yan sanda.
Hukumar kwallon kafa ta Ingila na shirin tattaunawa da kungiyoyin biyu da alkalin wasan Anthony Taylor da kuma 'yan sanda.
Al'amarin dai ya faru ne lokacin da dan wasan tsakiya na United Fred ya je dauko kwana bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai aka jefe shi da wani abu daga cikin 'yan kallo.
Bayan wasan, Fred ya ce: "Ban dauki abin a bakin komai ba lokacin da nake cikin fili, inda ya faru nan na bar shi, Wasu har nuna mani mutumin da ya yi jifan suka yi."
Dabi'un da ba a amince da su ba
Kocin Man United Ole Gunnar Solskjaer ya ce: "Fred da Jesse Lingard sun je dauko kwana abin ya faru, na ga hoton bidiyon, na kuma ji daga bakin yaran."
Ya ce halayyar da magoyin bayan ya nuna, wanda kyamara ta nuna "ba za a yarda da ita ba."
A wata sanarwa, Manchester City ta ce tana aiki da jami'an 'yan sanda domin gano masu laifin.
Ta kara da cewa, kulob din na ci gaba da bincike game da abin da aka wurgo cikin fili yayin wasan.
"Kungiyar na da tsarin kin amince wa da duk wani abu da ya shafi nuna wariya ko makamancin hakan, kuma duk wanda aka kama da laifin nuna wariya za a kore shi daga kungiyar har abada."
Sufuritanda Chris Hill ya ce, "Ina fatan matakin da muka dauka zai nuna yadda muka dauki lamarin da muhimmanci."
Hakan na zuwa ne shekara guda bayan da wariyar da aka nuna wa dan wasan Man City Raheem Sterling ta ja hankali a filin wasa na Stamford bridge.
Hakan ya kai ga dakatar da magoyin bayan Chelsea daga shiga filin wasan na tsahon rayuwarsa.
Fred ya ce, wannan abin da ake zargin ya faru ranar Asabar "ya nuna har yanzu muna cikin wata al'umma mai cike da koma baya."











