Premier League: Man United ta doke Man City a wasan hamayya

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta casa Manchester City har gida da ci 2-1, ta kuma koma matsayi na biyar a gasar Premier.
Wannan ne karon farko da aka doke Man City da kwallo biyu har gida tun da Pep Guradiola ya zama kocinta.
A minti na 22 ne da fara wasan Banardo Silva ya doke Rashford a cikin yadi na 18, abin da ya sa alkalin wasa ya bayar da finareti bayan duba na'urar VAR.

Asalin hoton, Getty Images
Rashford ne ya buga finaretin ya kuma ci a daidai minti na 23 wadda ita ce kwallonsa ta 10 a gasar Premier ta bana.
A minti na 29 kuma Anthony Martial ya kara kwallo ta biyu a ragar City, wanda hakan ya sa United ta ja ragamar wasan har aka juya hutun rabin lokaci.
City ce ta fi rike kwallo a wasan duka amma yawan kai hari da kuma saurin zuwa raga United ta fi.
Ana saura minti biyar a tashi daga asa Nicolas Otamendi ya ci wa City kwallon daya da ta samu, bayan wani bugun kwana.
Man United ta doke Tottenham da Man City a mako guda, maki shidan da ta samu ya ba ta damar matsawa kusa da gurbin shiga gasar Champions League, inda yanzu take ta biyar da tazarar maki biyar tsakaninta da Chelsea wadda ke ta hudu.
A tarihi, wannan ne wasan hamayyar Manchester na 149 a Premier - Man United ta ci 57, Man City ta ci 45, an yi canjaras 47.
Yanzu Liverpool ta bai wa Man City tazarar maki 14, kuma a tarihin Premier babu wata kungiya da ta taba lashe gasar idan har ta saman teburi ta ba ta tazarar maki 14.

Asalin hoton, Getty Images
Kazalika, makin da Guardiola ya samu a wannan kakar shi ne mafi karanci a cikin wasa 16 na farkon kaka tun sanda ya fara aikin horarwa - maki 32.











