Premier League: Newcastle ta rike wa Man City wuya

Tawagar Man City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maki 11 tsakanin Liverpool da Man City

Tawagar Pep Guardiola ba ta iya samun nasara kan Newcastle masu masaukin baki ba duk da irin wasan da ta buga, inda wasa ya tashi 2-2 a filin wasa na St. James' Park.

Manchester City ce ta rike kashi 77% na wasan amma Newcastle ta nuna cewa a gidanta ake yin sa, inda Willems ya farke kwallon da Sterling ya ci cikin minti biyu kacal - bayan minti 22 da fara wasa.

Ana saura minti takwas a tashi daga wasan ne kuma Kevin De Bruyne ya kara ta biyu.

Nan take Newcastle ta yi wani babban yunkuri ta kafar Shelvey, inda ya shauda kwallo cikin ragar City ana saura minti biyu a tashi daga wasan, bayan wani bugun tazara da aka yaudari 'yan wasan City - maimakon a buga cikin raga sai aka bai wa Shelvy fasin.

Duk da canjaras din, Man City ta koma ta biyu a teburi amma fa kafin Leicester ta yi wasanta a gobe Lahadi.

Yanzu tazara tsakanin Liverpool da City ta zama maki 11 kenan.

Hakan ba zai yi wa mai horarwa Guardiola dadi ba musamman ganin yadda muke tunkarar watan Disamba, inda za a fara wasanni ba ji ba gani kuma kungiyoyi da dama za su san matsayinsu.