Makomar Mbappe, Ronaldo, Benzema, Xhaka, Pochettino da Matic

Real Madrid na nazarin ware kudi fam miliyan 340 domin karbo dan wasan Paris St Germain mai shekara 20 Kylian Mbappe. (Le Parisien via Calciomercato)

Lyon na son dan wasan Real Madrid Karim Benzema, mai shekara 31, domin ya kammala rayuwarsa ta tamaula a kulub din da ya fara taka leda. (Mundo Deportivo, in Spanish)

Juventus ba za ta ci tarar Cristiano Ronaldo ba bayan ya fusata saboda an cire shi a wasa, sai dai ana sa ran zai nemi gafarar 'yan wasa. (Gazzetta dello Sport, in Italian)

Barcelona na sha'awar dan wasan gaba na Salzburg mai shekara 19 Erling Braut Haaland a matsayin wanda zai maye gurbin Luis Suarez. (ESPN)

Dan wasan Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 27, yana son komawa Italiya a yayin da AC Milan ta fara nuna sha'awar dauko shi a watan Janairu bayan tube shi daga Kyaftin din Arsenal.(RSI via Star)

Tottenham ta koma kan dan wasan RomaLorenzo Pellegrini, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin Christian Eriksen. (Football Italia)

Nemanja Matic na son barin Manchester United a farkon watan Janairu, kuma akwai yiyuwar ya koma Italiya. (Telegraph)

Akwai yiyuwarTottenham za ta iya raba gari da kocinta Mauricio Pochettino idan har kungiyar ta sha kashi a hannun West Ham. (Telegraph)

Pep Guardiola, wanda ya shafe kaka uku a Bayern Munich kafin ya koma Manchester City, akwai yiyuwar zai sake komawa Jamus domin maye gurbin Niko Kovac da aka kora. (The Athletic, subscription required)