Mesut Ozil zai koma gida, Solskjaer ya ci banza

Manchester United ta kammala cimma yarjejeniya ta baka domin sayen dan wasa dan kasar Croatia, Mario Mandzukic, mai shekara 33, daga kulob din Juventus a wannan shekarar. (Tuttosport, via Mirror)

Da alama babu wata guguwa da za ta ci kocin Manchester United din Ole Gunnar Solskjaer ko da kuwa kulob din bai yi nasara ba a wasan da zai taka da Liverpool nan gaba ba. (Times - subscription required)

Lyon ta gaza daukar tsohon kocin Chelsea da Manchester United, Jose Mourinho a matsayin sabon manaja, wanda suke ganin samun sa zai ba su damar koma wa gasar Premier League. (Mirror)

An tabbatar da tattaunawar da ke gudana tsakanin Fenerbahce na Turkiyya da Arsenal wajen sayen Mesut Ozil, mai shekara 30, a watan Janairu. (Takvim, via Sun)

To sai dai an ce Ozil na fargabar cewa taka ledarsa a Arsenal ta kawo karshe. (Mirror)

Mai tsaron bayan kungiyar ta Arsenal, Shkodran Mustafi ya ce 'sukar sa da ake yi ta wuce kima, inda kuma dan wasan mai shekara 27 zai iya barin kulob din zuwa wasu da suka hada da kulob-kulob a Bundesliga (Der Speigel , via Guardian)

Manchester United na son dan wasan Benfica, Ruben Dias to amma kulob din zai bai wa dan wasan sabuwar kwantaragin da za ta sa darajarsa ta karu zuwa fam miliyan 79. (Express)

Real Madrid za ta fara tattaunawa da Tottenham domin ganin ta sayi Christian Eriksen mai shekara 27 a watan Janairu mai kamawa. (Marca)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce kulob din ba zai sayar da dan wasan tsakiya na kasar Ingila na 'yan kasa da shekara 21, Phil Foden, mai shekara 19 ba koda kuwa an yi musu tayin fam miliyan 450. (Sun)

Dan wasa dan kasar Uruguay na gaba Edinson Cavani, mai shekara 32, da kuma dan wasan kasar Brazil na baya Thiago Silva, mai shekara 35, za su iya barin Paris St-Germain ba tare da kwantaragi ba, a karshen kakar wasannin nan. (ESPN)

Dan wasan Barcelona na tsakiya, Ivan Rakitic, mai shekara 31, da ake dangantawa da Manchester United a bazarar da ta gabata ya nuna alamun zai sauya wani kulob din domin taka leda a babban kulob mai daraja ta daya. (Mail)