NFF da kulob din Roma sun kulla yarjejeniya

Asalin hoton, NFF
Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya NFF ta kulla yarjejeniyar aiki tare da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma mai buga gasar Serie A ta Italiya.
Bisa ka'idojin yarjejeniyar, Roma da NFF za su rika gudanar da harkokin da suka shafi wasanni a ciki da wajen fili, kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana ranar Juma'a.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Bangarorin biyu za su rika taimaka wa juna wajen ci gaban harkokin wasanni da suka hada da shawarwari game da horar da matasan 'yan wasa daga Najeriya da kuma koyar da kulob-kulob a Najeriya yadda za su rika tafiyar da shafukansu na sada zumunta.
Ita kuma NFF za ta taimaka wa Roma wajen gina nata harkokin a Najeriya.
Kazalika, a watanni masu zuwa jami'an hukumar ta NFF za su yi tattaki zuwa birnin Rome domin ganin yadda kungiyar matasa ta Roma ke gudanar da wasanninsu.
Hakan zai ba su dama wurin gina matasa da kuma kungiyoyinsu a harkar wasanni a gida Najeriya.
Shugaban kungiyar ta Roma Jim Pallotta ya ce tun a 2018 suka fara aiki da Super Eagles yayin gasar cin Kofin Duniya a kasar Rasha.
"Rukunin ma'aikatanmu sun fara aiki tare da Super Eagles a 2018 a shafukan sada zumunta da kuma lokacin gasar Kofin kasashen Afirka, wanda aka fara da maudu'in #ForzaSuperEagles.
"Mu ne kungiya ta farko daga wajen Najeriya da ta bude shafin Twitter cikin harshen Pidgin mai shelkwata a Lagos."
Kungiyar za ta duba yiwuwar buga wasan bude ido a Najeriya tare da bude makarantar horar da wasanni.











