Chelsea: Matashin dan wasa Mason Mount zai yi jinya

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea za ta yi jiran kwana biyu kafin sanin irin halin da matashin dan wasanta mai tashe Mason Mount yake ciki bayan ya fice daga wasan da Valencia ta casa ta da 0-1 a daren Talata a Champions League.
Koci Frank Lampard ya tabbatar da cewa Mount, dan shekara 20, ya ji rauni a idon-sawunsa bisa wata gamuwa da suka yi da Francis Coquelin.
Dan wasan tsakiyar ya fara dukkanin wasan da Chelsea ta buga a Premier ta bana, inda ya zura kwallo uku a wasa biyar.
Sannan kuma ya fara murza wa kasarsa ta Ingila kwallo a farkon wannan watan.
"Za mu duba abin da ya faru nan da sa'o'i 48 domin sanin takamaiman abin da ya faru," in ji Frank Lampard.
"Ba mu san girman raunin ba. Idon-sawunsa ne kiuma ba mu ji dadi ba domin yana buga wasa mai kayatarwa kuma daren yau (jiya Talata) ma ya fara wasan da kyau."
Mason Mount ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a watan Yuli kuma ya fara wasa a Chelsea tun a ranar farko da aka fara kakar bana.







