Liverpool: Tataburzar da ake sha wajen kare kambun Champions League

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Tom Rostance
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta fara dandana wuyar kare kofinta na Zakarun Turai, na Champions League a karo na uku a ranar Talata, inda ta sha kashi 2-0 a hannun Napoli.
Liverpool masu rike da kofin nahiyar Turai - kuma wadanda suka zo na biyu a 2018 - na fatan buga wasanni 13 a gasar da aka fara zuwa ranar 30 ga watan Mayu 2020 da za a yi wasan karashe a birnin Santanmbul, inda kungiyar ta kafa wani tarahi shekara 14 da suka wuce.
Mene ne wahalar kare kofin Champions League? Shin kare kofin na iya zama hakura da daya muhimmin abu a Anfield - wato nasarar cin gasa ta farko a cikin karni?
Yaya wuyar take?
Da babu wahala da kowace kulob ta yi. Hatta manyan kulob na wannan zamani sun gagara kare kofin Champions League din da suka ci.
Kafin Zinedine Zidane ya kai Real Madrida ga cin kofin sau uku a jere a 2016, 2017 da 2018, ba wani kulob da ya taba cin kofin a jere, tun sadda kwallon da Frank Rijkaard ya ci a raga a Vienna, wanda ya kai AC Millan karkashin Arrigo Sacchi ga samun irin wannan nasara a 1990.
Hatta kungiyar Barcelona ta Pep Guardiola- daya daga cikin manyan kulob a wannan karnin - da kyar ta iya cin kofin Champions League sau biyu a jere, cikin shekaru 2.
Duk da haka Barcelona bata samun nasara a wasan karshe cikin shekarar biyu a jere ba.
Tun 1956 da aka fara gasar cin kofin nahiyar Turai, kungiyoyi 11 ne suka taba kaiwa wasan karshe a jere.
Kuma shekara 30 na farko wasu kungiyoyi ne suka mamaaye shekaru 30.
Liverpool ce kadai kungiyar da ta samu nasarar kaiwa wasan karshe har sau uku, a cikin kungiyoyin.
Valencia kuma ta samu kaiwa wasannin karshe a jere ba tare ta yi nasara a duka wasannin ba.
Ita kuma Real Madrid sau biyar tana kaiwa wannan matakain a shekarun farkon gasar ba tare da wani babban kalubale ba.
Yadda masu rike da kofin ke fama
Tun 1992 da aka fara gasar Champions League, kulob mai kare kofinsa daya ne kadai ya tsallake matakin rukuni.
Wani abin kunya kuma shi ne yadda kungiyar Chelsea ta kasa iya shiga gasar watanni shida bayan ta ci kofin a 2012.
Alamu sun nuna kungiyar Blues ta Roberto din Matteo ta yi rashin sa'a.
Duk da cewa ta samu maki 10 da take nema, kwalle biyun da Shakhtar Donetsk suka zura wa Blues din a Stanford Bridge ya sa kungiyar ta ci kasa.
A 2013 wanda ya ci kwallayen, Willian ya koma Chelsea.
Haka kuma za a yi mamaki idan Liverpool ta kasa tsallake matakin rukuni a Group E, inda za ta fuskanci Napoli da kuma Red Bull Salzburg da kuma Genk.
Sai dai kuma da kyar kungiyar ta tsallake matakin rukuni a kasar 2018.
Liverpool na bukatar ta doke Napoli akalla da ci daya da babu, ko kuma kwallaye biyu, kafin ta samu kaiwa mataki na gaba.
Kungiyar ta riga ta samu nasarar da ci daya da babu, bayan Allisson ya zura kwallo a ragar Napoli, ana dab da karshen wasan.
Da zarar tsallake wannan, abun jira a gani shi ne yadda za ta kaya - amma a shekara 10 da suka gabata, sau shida kungiyoyin da suka kai wasan karshe suka samu kaiwa matakin 'yan takwas.
Karo biyar ana lallasa su a wasan dab da na karshe, sau hudu kuma suna cin gasar.
Shin tana shafar makomar gasar?
Tun 1990 Liverpool bata ci gasar ba. Za su shi makon farko na Champions League da akalla maki biyar, a matsayin wadanda ke kan gaba a gasar Premier League.
Shin za a iya mayar da hankali a kan duka biyun?
Tarihin baya-bayan nan ya nuna haka. Idan a nahiyar Turari akwai kungiyar da ta fi kowacce, to a cikin kasa ma a kwai kungiyar da ta fi saura.
Shekara goma baya, sau biyar kungiyoyin da suka ci Champions League na cin gasannin kasashensu.
Barcelona sun yi fice da hakan - a sadda suka ci gasanin Champions League biyar - su suka ci La Liga.
Gudanar da 'yan wasa na da muhimmanci. Bayan cin Newcastle a ranar Asabar, ya yayyafa tambayar da ka yi masa ta neman jin ko Klopp shin zai kara azama domin cin gasar wannan shekara, ruwan sanyi.
Ya zabi ya fara wasan ba tare da keftin Jordan Henderson da dan wasan gaba Roberto Firmino a wasansu da Magpies.
Shin daya idon nasa na kan Napoli?
"Ko akwai shawarar yadda za a canza?" Klopp ya tambaya. Ina so in san me za mu yi? Ba ma kawo wani sauyi a tsakanin gasanni. Ba mu taba ba. Magana ce ta abun da ya samu ne, wa ke yin me - haka muke yanke shawara idan za mu iya."
"Gaskiya a yawancin lokuta ba mu iya yin canji da yawa. Dole mu sa wadanda za su iya aiki. Ba za mu je wasa da Napoli mu buga kashi 60 ko 70 ko 80 na abun da muka saba bugawa ba. Abin takaicin shi ne sun iya wasa sosai. Su ne irin abokan adawa da suka dace. Sun sha ba mu wahala kuma yanzu akwai bukatar mu tabbatar da cewa matsalar bata taka kara ta karya ba.
Kaiwa wasan karshe da suka yi a Madrid bara bai shafi Liverpool a gasar ba. Duk da haka sun samu maki 97 kuma sau daya kacal suka sha kaye a kakar.
Sun ci 10 cikin wasanninsu 12 a gasar Premier bayan gasar nahiyar Turai, amma sun yi rashin sa'ar kasancewa a Anfiels a wasanni takwas, ciki har da guda shida a matakin rukuni.
A bana, Liverpool din za su buga wasanni biyar a gidansu bayan wasanni shida a matakin rukuni a Champions League.
A karshen mako mai zuwa Liverpool za ta yi wasa a Chealsa, wanda kuma shi ne kadai wasan da za karbi bakuncinta.
A hannu guda kuma, a kakannin wasanni biyu da suka gabata, shida daga cikin wasanni 12 na Manchester City a matakin rukuni, an karbi bakuncinsu ne.
Yayin da za su iya cin gajiyar ziyarar da za su kai, Liverpool na da wasannin da za ta yi da Chelsea da Tottenham - waadda ta zo ta biyu a shekarar da ta gabata - da kuma Manchester City da zarar an kammala gasar nahiyar Turai.
Don haka, da sauran rina a kaba.











