Neymar ya yi kuka da idonsa bayan ya kasa barin PSG

Neymar Junior

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Neymar ne dan wasa mafi tsada a duniya

Bayan watanni da aka dauka ana sa-toka-sa-katsi da kuma ka-ce-na-ce yanzu dai mun ga karshen abu. Neymar zai ci gaba da zama a Paris St-Germain.

Yayin da kura ke lafawa, ya kamata mu sani cewa ba Neymar ne wanda abin ya fi bai wa mamaki ba - duk da kokarin da ya yi na barin kungiyar, ya kwana da sanin cewa wannan cinikin ba mai yiwuwa ba ne.

Gidan rediyon El Chiringuito na kasar Portugal ya ruwaito cewa Neymar ya yi kuka da idonsa bayan an shaida masa cewa ba zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Bercelona ba.

Babban abin da ake nema yayin kulla yarjejeniyar ciniki - a harkar kwallo ko kuma a ko'ina - shi ne ko dai a samu mai zumudin saya ko kuma mai zumudin sayarwa, ko kuma in so samu ne a samu duka.

Sai dai a wannan yanayin, ita Bercelona ta yi zargin cewa zakarun na Faransa tun asali ba su da niyyar sayar da dan wasan, yayinda ita kuma PSG tana zargin cewa Berca ba tun farko dama bata yi niyyar sayan dan wasan ba ne.

Wannan rashin yardar shi ne abin da ya gurgunta tattaunawar tun daga farkonta.

Ta yaya aka zo nan din?

A watan Afrilun da ya gabata dan wasan na Brazil ya fara tattaunawar tsawaita yarjejeniyar sa a PSG.

Sai aka yi rashin sa'a dan wasan ya gamu da wasu abubuwa da suka kawo masa cikas, wadanda ake ganin sun hana masa jin dadin zama a birnin na Paris.

kamar yadda rahotanni suka bayyana, PSG ta kasa cika wasu daga cikin alkawuran da ta yi masa, wadanda suka hadar da rashin daukar mataki kan ihu daga wasu daga cikin magoya baya, rikici tsakaninsa da dan wasan gaba Edinson Cavani kan wanda zai rika buga fanareti, rarrabuwar kai a tsakanin 'yan wasan kungiyar da kuma jin cewa alkalan wasa ba sa ba shi kariyar da ta dace.

A watan Janairu ne dan wasan Strasbourg mai suna Anthony Goncalves ya yi masa keta har sau uku a jere, wadanda duka sun cancanci a ba shi katin gargadi (amma ba a ba shi ba) wanda hakan ya tilasta wa Neymar tafiya jinya da kuma hutun wasanni har 18.

Waye zai ki Paris? - tabbas Neymar yana son Paris - shi ya sa ma har ya fara tunanin tsawaita zamansa a birnin duk da irin shakkun da yake da shi na abin da ka iya faruwa da kuma kawa-zucin koma wa Berca da ya yi na dan wani lokaci.

kawai kuma sai wani abu ya faru jim kadan bayan Bercelona ta yi rashin nasara a hannun Liverpool a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar zakarun turai (Champions League) a watan Mayu.

Shugaban Bercelona Josep Maria Bartomeu ya shaida wa Masu daura wa kungiyar kaftin - Lionel Messi da Gerard Pique da Sergio Busquets da Sergi Roberto da kuma Luis Suarez - cewa ba wai kawai zai sayo Neymar ba ne, yana da kwarin gwiwar cewa dan wasan zai dawo.

Wadanda Neymar yake mu'amala da su a birni na Bercelona irin su Messi da Pique da Suarez sun shaida wa Neymar cewa cinikin zai yiwu kuma lallai suna bukatarsa a Berca domin su lashe gasar Champions League.

Neymar ya yi sha'awar hakan sosai domin dai dama yana ta tunani kan matakin da ya dauka na barin Berca tun farko.

Kazalika, Messi ya yi tunanin cewa, ganin yadda ya fara manyanta, Neymar zai iya jagorantar kungiyar nan da 'yan shekaru.

Daga nan ne fa aka saka zare!

A daidai wannan lokaci, an shaidawa manyan 'yan wasan Barcelona cewa kulob din bai sayi Antoine Griezmann ba daga Atletico Madrid - sai dai Atletico din ta bayyana cewa ta ga wasu takardu da ke nuna cewa an kammala yarjejeniyar tun a watan Maris.

Matsalar da aka kara samu kuma ita ce, mutane da dama har a birnin Paris din sun zaci cewa Barcelona ba ta da sauran kudi tunda suna zaton ta sayi Griezmann.

Barcelona sai da ta ciyo bashin yuro miliyan 35 daga banki domin sayen dan kasar Faransar.

Saboda haka za ka sha mamakin matsalar tattalin arziki da kungiyar za ta shiga da ta sayi Neymar.

Ganin cewa babu wata takamammiyar magana daga mahukuntan PSG, Neymar ya fara tunanin yarjejeniyar ba mai yiwuwa ba ce har ma ya hadu da jami'an kungiyar kuma ya fada masu cewa zai buga wasan farko na Ligue 1.

Kwana daya kafin wasan daraktan wasanni Leonardo ya bukace shi da ya shaida wa duniya cewa ba zai bar PSG ba.

Neymar bai aminta da hikimar yin hakan ba kuma ya fada masu cewa ya yarda zai yi wasa amma bai shirya yin waccan sanarwa ba.

Su kuma tsofaffin abokan wasansa a Barcelona suna ta turo sakonnimn cewa ya kara hakuri za a cimma yarjejeniya.

Karshe dai maganar daya ce kacal: idan Barca na son Neymar sai ta amayo yuro milyan 215. Daga baya ta fada wa PSG cewa za ta hada da 'yan wasanta.

Sai a ranar 27 bga watan Agusta ne Barcelona ta mika tayin a hukumance na yuro miliyan 115 lakadan sai alawus-alawus na miliyan 13.5 da kuma 'yan wasa uku.

ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce to ta na son Jean-Clair Todibo da Ivan Rakitic sai kuma Ousmane Dembele a matsayin aro.

Jean-Clair Todibo da Ivan Rakitic sun nuna dari-dari da komawa birnin Paris da tak-leda. Shi kuwa Dembele nan take ya ce a'a.

Tattaunawa ta kakare ne bayan da PSG ta bukaci Barca ta biya yuro miliyan 15 a matsayin alawus. Bayan Barca ta yarda za ta biya sai kuma suka ce suna bukatar yuro miliyan 150 maimakon 130 da kuma alawus.

Neymar ya ce babu matsala zai biya yuro milyan 4 daga aljihunsa. Mintun kadan kuma sai jami'an PSg suka shaida masa cewa hukumar kwallon kafar Faransa ta French Football Federation ta haramta wa 'yan wasa biyan irin wadannan kudi.

Ana haka ne kuma, Real Madrid - wadda dama ba ta nuna wata sha'awar kirki ba kan dan wasan - ta mika tayin yuro miliyan 100 hadi da Gareth Bale da james Rodriguez da kuma Keylor Navas.

Albashin Bale bai bari an je ko'ina ba a tattaunawar. Ita ma Juventus ta miko tayin yuro miliyan 100 da kuma Paulo Dybala, abin da PSG ta yi watsi da su baki daya.

A karshe dai Neymar ya ce Sifaniya yake son komawa lokacin da aka tambaye shi game da barin PSG. Ya yi hakan ne saboda ya guje wa jin kunya domin ba shi da tabbas a lokacin ko wacce kungiya zai je tsakanin Madrid ko Barca.

Daga bisani Barcalona ba ta nuna wata sha'awa mai karfi ba ga Neymar domin kuwa Bartomeu, shugaban kungiyar, bai taba ganawa da shugaban PSG Al-Khelaifi ba ido da ido. Amma lokacin da Barca ke son daukar Frenkie de Jong daga Ajax da kansa ya je Netherlands domin tattauna yarjejeniyar daukarsa.

Ko ba komai dai yanzu Bartomeu zai ce "ai mun kokarta" idan wani ya tambaye shi, sannan kuma zai dadadawa wadanda suke cike da haushin Neymar kan yadda ya kai kulob din kara kotu har sau biyu.

Idan abubuwa ba su ta fi lafiya lau ba to shikenan sai a tari gaba. Sai dai kuma ba abin tayar da jijiyar wuya ba ne saboda yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da koci Tuchel kuma komai zai warware tunda kura na lafawa.