Abin da ya biyo bayan rufe kasuwar sayen 'yan wasan Turai

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kulob din PSG Nasser Al-Khelaifi zai bar Neymar ya koma Barcelona ne kawai idan da an kawo tayi mafi tsada a tarihi na yuro miliyan 300, a cewar rahoton Le Parisien.
A gefe guda kuma, L'Equipe ta ruwaito cewa babu mamaki Messi ne ya haddasa takaddama game da komawar Neymar din zuwa Barcelona a wani sakon tes da ya tura yayin da tattaunawa ta kakare tsakanin PSG da Barcelona.
Dan wasan gaban Borussia Dortmund na kasar Ingila mai shekara 19 Jadon Sancho ka iya koma wa Manchester United, inda ya ce "ba zai damu ba" idan ya koma kasarsa ta haihuwa, in ji Mirror.
Amurka na neman daukar kocin tawagar mata ta Ingila Phil Neville domin maye gurbin Jill Ellis, kamar yadda jaridar Mail ta ruwaito.
Manchester United ta tura wakilai zuwa kallon wasan Benfica da Braga a ranar Lahadi, inda za su saka ido kan 'yan wasa biyu wato Ruben Dias mai shekara 22 da kuma Florentino Luis mai shekara 20, a rahoton Mirror.
Kungiyar Almeria mai buga gasar Segunda ta Sifaniya ta sako Manchester United a gaba a shafukan sada zumunta bayan ta doke United din wajen daukar Arvin Appiah mai shekara 18 daga Nottingham Forest. (Sun)
Wani shafin magoya bayan Liverpool ya bukaci kulob din da ya sayar da Mohammed Salah mai shekara 27 domin tara kudin sayen Kylian Mbappe da Jadon Sancho na Dortmund ko kuma Kai Havertz mai shekara 20 daga Bayern Leverkusen. (Mirror)
Dan wasan gaban Atletico Madrid Nikola Kalinic mai shekara 31 ya koma Roma a yarjejeniyar aro, inda ita kuma Roman ta tura Patrik Schick mai shekara 23 aro zuwa RB Leipzig(Gazzetta dello Sport - in Italian).











