Har yanzu Neymar na fatan koma wa Barca, Kasuwar saye da musayar 'yan wasa
Fatan Neymar na koma wa Barcelona ya kara girma bayan Ousmane Dembele ya yarda a hada da shi a cikin yarjejeniyar da ta kunshi 'yan wasa uku tare da karin kudi.
Duka wannan ana fatan ya faru kafin nan da karfe 11:00 agogon Nijar da Najeriya, lokacijn da za a rufe kasuwar Faransa da kuma Sifaniya.
Tun farko dai Barcelona ta yi tayin bayar da Ivan Rakitic da Jean-Clair Todibo da Dembele da kuma karin fan miliyan 120 ga PSG.
Amma tattaunawa ta kakare bayan Dembele ya ki yarda a hada da shi a cikin yarjejeniyar.
Rakitic da Todibo tuni suka yarda su koma birnin Paris da taka-leda, inda rahotonni ke cewa har PSG din ta fara hada bidiyon sanarwa a farkon wannan makon.
Sai dai jaridar Mail ta ruwaito cewa Dembele ya sauya ra'ayi kuma yanzu ya yarda ya koma PSG din.
Jaridar L'Equipe ta yi ikirarin cewa tuni tattaunawa ta yi nisa bayan koci Thomas Tuchel na PSG ya shawo kan Dembele.
PSG tana sha'awar musayar amma ta janye daga tattaunawar ne bayan da aka janye sunan Dembele daga teburin tattaunawar.

Asalin hoton, Getty Images














