Chelsea ta bai wa Mallorca aron Baba Rahman

Baba Rahman

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron bayan Chelsea, Baba Rahman ya koma Real Mallorca, domin buga mata wasannin aro, bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar zama a Stamford Bridge.

Rahman wanda ya koma Blues daga Augsburg a kakar 2015, zai ci gaba da zama dan kungiyar ta Stamford Bridge har zuwa karshen kakar 2022.

Kamar yadda Chelsea ta sanar a shafinta na Intanet ta ce dan kwallon zai buga wa Mallorca wasannin aro har zuwa karshen kakar bana.

Rahman mai shekara 25 dan kwallon tawagar Ghana ya yi wasannin aro a Schalke 04 ta Jamus da Reims ta Faransa.

Dan wasan ya fara buga wa Chelsea wasa a karawar da ta doke Maccabi Tel Aviv a gasar Champions League a watan Satumbar 2015, jumulla ya buga mata karawa 23.

Mallorca ta koma buga gasar La Liga a bana, bayan da ta yi nasara a wasannin cike gurbi da ta yi.