Gwarzon FIFA: Van Dijk da Messi da Ronaldo

Fifa Award

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana 'yan wasa uku da za a zabi gwarzon dan kwallon kafa na duniya na bana.

Cikin 'yan wasan sun hada da Virgil Van Dijk na Liverpool da Netherlands da dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo na Portugal da dan wasan Argentina, Lionel Messi na Barcelona.

Van Dijk ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Turai na shekarar nan, kuma shi ne wanda ya fi taka rawar gani a Premier, kuma wanda kungiyar kwararrun 'yan wasa ta karrama.

Shi kuwa Ronaldo ya lashe kofin Serie A a kakar farko da ya fara buga wa Juventus tamaula, kuma shi ne dan kwallon da babu kamarsa a gasar da aka kammala.

Haka kuma Ronaldo ya jagoranci tawagar kwallon kafa ta Portugal lashe UEFA Nations League a watan Yuni, sannan shi ne dan wasan da ya fi yin fice a gumurzun.

Shi kuwa Messi ya ci kofin La Liga a Barcelona kuma karo na 10, sannan shi ne dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar nahiyar Turai a kakar bana.

Haka kuma FIFA ta bayyana sunan mata uku da nan ma za a fitar da wadda ta fi taka-rawar gani a shekarar nan.

Ciki har da 'yar wasan tawagar Amurka Megan Rapinoe wadda ta ci kofin duniya da takalmin zinare da kyautar wadda ta fi yin bajinta a kofin na duniya da aka yi a Faransa.

Sauran sun hada da Alex Morgan da kuma Lucy Bronze ta Ingila.

Ranar 23 ga watan Satumba a birnin Milan za a gudanar da bikin karrama wadan da suka yi bajinta a fagen tamaula a bana.