Mannchester City na son Sane, Atletico na son Eriksen

Leroy Sane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yanzu haka Leroy Sane na jinyar rauni a gwiwarsa

Bayern Munich, in ji jaridar Sun, ta farfado da sha'awarta ta daukar dan wasan Manchester City Leroy Sane a watan Janairu duk da cewa dan shekara 23 din yana fama da rauni a gwiwarsa.

Ita ma Juventus za ta yi kokarin sayar da dan wasan gabanta Mario Mandzukic mai shekara 33 da kuma na tsakiya Emre Can dan shekara 25 a kasuwar watan Janairu idan an bude, a cewar rahoton Goal.

Bercelona ba ta iya daukar Lucas Moura mai shekara 27 daga Tottenham ba ne saboda ta kasa biyan fan miliyan 45 na farashinsa da Tottenham din ta nema, kamar yadda Mundo Deportivo ta ruwaito.

Kungiyoyin Real Sociedad da Athletic Bilbao za su yi kokarin daukar dan bayan Chelsea Cesar Azpilicueta mai shekara 30 idan ya nemi ficewa daga kulob din. (Express)

Ita kuwa Atletico Madrid tana ta daura damarar daukar dan wasan tsakiyar Tottenham ne Christian Eriksen mai sherkara 27, inda za ta kai tayi mai tsoka, in ji jaridar AS.

Gidan rediyon El Chiringuito na kasar Portugal ya ruwaito cewa Neymar ya yi kuka da idonsa bayan an shaida masa cewa ba zai koma Bercelona ba.

Shi ma Luis Suarez na Bercelona ya ce Neymar ya yi iyakar kokarinsa domin ya bar Paris St-Germain, in ji Fox Sports.

Nemanja Matic na Manchester United ya ce kocinsu Ole Gunnar Solskjaer ne zai dauki alhaki idan kulob din bai tabuka ba a kokawar neman lashe Premier ta bana. (Times)