Yadda ciniki ya kasance a kan Dybala, Coutinho, Ozil, da Eriksen

Neymar Jr

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, PSG ta yarda da sayar wa Man United ko wasu kungiyoyin Neymar amma ba dai Barcelona ba

Ciniki ya fada tsakanin Tottenham da Juventus na sayen dan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, mai shekara 25, a kan kudin da ya kai fan miliyan 62, kamar yadda labari ya bayyana ta (Sky Sports Italia, via Daily Mail)

Yanzu Dybala zai fara tattauna yadda kwantiraginsa zai kasance da Tottenham kafin karshen wa'adin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta Ingila ranar Alhamis in ji (Goal)

Baya ga wannan kuma har yanzu Tottenham din na sha'awar sayen dan wasan Barcelona na Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 27, yayin da wani rahoton ke cewa Arsenal ba ta taba nuna sha'awarta da shi ba, in ji (ESPN)

Ita kuwa kungiyar Amurka ta DC United rahotanni na cewa tana shirin tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 30, domin maye gurbin Wayne Rooney wanda zai tafi Derby, kamar yadda jaridar (Mirror) ta ruwaito.

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ozil ya koma Gunners daga Real Madrid a shekarar 2013

Manchester United ta kara azama domin ganin ta sayi dan wasan tsakiya na Tottenham kuma dan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, kamar yadda jaridar (Telegraph) ta labarto.

Eriksen ba ya daga cikin jerin 'yan wasan da kociyan kungiyar ta Tottenham, Mauricio Pochettino, yake shirin amfani da su a nan gaba, kuma ya fitar da shi daga tsarinsa tun lokacin da dan wasan ya nuna cewa yana son sauya sheka, in ji (Mirror).

United ta bullo da maganar neman sayen Eriksen ne sakamakon rashin tabbas na kasancewar dan wasanta na tsakiya, dan Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, na ci-gaba da kasancewa a kungiyar har zuwa karshen kasuwar yanzu, in ji (Standard).

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce hankalin Paul Pogba ya bar Manchester United

Haka kuma United din na duba yuwuwar daukar tsohon dan wasan Tottenham na gaba Fernando Llorente, kasancewar dan wasan na Sifaniya mai shekara 34 a yanzu ba shi da wata kungiya kamar yadda (Sky Sports Italy, via Metro) suka ruwaito.

Ita kuwa kungiyar Manchester City za ta tabbatar da sayen Joao Cancelo ne daga Juventus a ranar Laraba, bayan da dan wasan na baya mai shekara 25, na Portugal ya tsallake gwajin lafiyar da aka yi masa, in ji (Star).

Tayin da Arsenal ta yi wa matashin dan wasan baya na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 20, na kungiyar RB Leipzig ta Jamus, na fan miliyan 55 bai samu karbuwa ba a wajen kungiyar ta gasar Bundesliga, a labarin da (Bild) ta ruwaito.

RB Leipzig ta gaya wa Arsenal din cewa ba ta da niyyar sayar da Upamecano, wanda a kwantiraginsa yake da damar barin kungiyar ta Jamus idan aka samu mai sayensa fan miliyan 92, a wani labari da (Mirror) ta yi.

Ita kuwa kungiyar Paris St-Germain ta yi tayin sayar da dan wasan gaba na Brazil ne Neymar, mai shekara 27, ga Manchester United, ko Juventus ko kuma Real Madrid, amma ban da tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, a labarin da (Sport) ta ruwaito.

Dan wasan Manchester United na Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 26, bai koma atisaye ba da manyn 'yan wasan kungiyar sakamakon rade-radin da ake yi na yuwuwar barinsa kungiyar ta Premier, a wani labari da jaridar (Mirror) ta rubuta.